Labaran Duniya

Tabbas ba’a gadon ilmi, amma da ana gadon sa sai muce malama Zainab Ja’afar ta gaje shi.

Tabbas ba’a gadon ilmi, amma da ana gadon sa sai muce malama Zainab Ja’afar ta gaje shi.

Domin mahaifin ta Sheikh Ja’afar ba’a sanshi da komai ba, illa dan gan takarshi da littafin Allah, wajen fassara shi, da kuma karanta tashi, wannan aiki yakeyi har zuwa karshen nunfashin sa a duniya littafin Allah ne a harshen sa.

To haka matansa basu da wani abu illa karantar da wannan littafi na alkur’ani, ai malam daga jin tarihin wannan gidan kasan tabbas Allah zai albarkaci, zuri’ar wannan gidan.

Dan haka wannan aiki da wannan baiwar Allah, ta dukufa tanayi gado ne daga kowani janibi, sannan gashi iyayen ta, sun damka amanarta ga bawan Allah makiya da masoya an hadu akan nagartar sa, da ilmin sa.

A zahirin gaskiya duk Nigeria zaiyi matukar wahala a iya cire kalarta, guda goma, ace a samu uba kamar nata haka miji da uwa, dama ita kanta.

Kawai malama Zainab Ja’afar Mahmud kiyi ta tasbihi, domin Allah yayi miki ni’ima babba, kuma duk wata ni’ima akwai mai hassada, kuma iya girman ni’imar ka iya girman mahassadanka.

Ina fatan Allah ya karfafeki akan wannan aiki, shi kuma mai gidanki, Allah ya bashi ikon karfafanki akan ayyukan alheri.

Muhammad Ismail Ali.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button