Labaran Duniya

WATA SABUWA: An Ba Wa Musulmai Wa’adi Su Cire Lasifika A Masallatai A India

WATA SABUWA: An Ba Wa Musulmai Wa’adi Su Cire Lasifika A Masallatai A India

Shugaban Jam’iyyar Maharashtra Navnirman Sena (MNS) Raj Thackeray ya ce ba ya son tashin hankali a Maharashtra. Don haka ya ce Musulmi su fahimci babu addinin da ya fi ƙarfin doka, kamar yadda BBC ta rawaito.

Ya ce buƙatarsa ta cire lasifika daga Masallatai ba ya nuna adawarsa ba ne ga Sallar da Musulmi suke yi, kuma haka jam’iyyarsa ba ta son tashin hankali.

An ba Musulmi wa’adi su cire lasifika a Masallatai a Maharashtra zuwa ranar 2 ga watan Mayu. “Zuwa 3 ga Mayu za a ga abin ya kamata a yi.”

“Idan har ba a cire Lasifika a Masallatai ba zuwa 3 ga Mayu, to ma’aikatan MNS za su yi amfani da lasifika suna rera Hanuman Chalisa a Masallatan”.

Rikicin addini a Indiya tsakanin Musulmi da Hindu na ƙara ƙamari, lamarin ya munana a cikin ‘yan shekarun nan, sakamakon yadda ‘yan Indiya ke jifan juna da kalaman kiyayya.

Muna matukar godiya da bibiyar mu a kowane lokaci a tashar Mai albarka ta hausablogng

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button