MATALAR SAƁANIN GANIN WATA A NAGERIYA WA YA KAMATA AL’UMMA SU BI ?

MATALAR SAƁANIN GANIN WATA A NAGERIYA WA YA KAMATA AL’UMMA SU BI ?
– DAGA Bashir Abdullahi El-bash
Mai alfarma sarkin musulman Nageriya, Alhaji Sa’ad Abubakar III, ya ba da sanarwar cewa ba su samu labarin ganin watan Shawwal ba yau a Nageriya, saboda haka gobe za a sake tashi da azumi ya zama an cika talatin, jibi a yi sallah.
Sai dai kuma, fitaccen Malamin addinin musulunci, kana shugaban ɗarikar Tijjaniyya a Nageriya, Shaikh Ɗahiru Usman Bauchi shi kuma a nasa ɓangaren ya ba da sanarwar cewa an ga jinjirin watan na Shawwal, saboda haka gobe za su ajiye Azumi, jibi kuma za su yi sallah.
Matsalar saɓanin ganin wata dai a Nageriya da ma sauran ƙasashen musulmai a Afrika ba sabon abu ba ne musamman a lokacin fara azumi da sallah, kuma ba wannan ne farau da Shaik Ɗahiru Bauchi da wasu ke saɓawa fadar mai alfarma sarkin musulmai kan ganin wata ba.
Sarkin musulmai dai a hukumance shi ne shugaban musulman duk Nageriya na kowacce ɗariƙa kamar Izala, Ɗariƙa, Tijjaniyya, da ma Shi’a da sauransu, shi kuma Shaikh Ɗahiru Bauchi Uba ne kuma shugaba ne na wata ƙungiyar rukunin wasu al’umma cikin musulman Nageriya.
Shin a mahanga ta addini wane ne wanda ya fi dacewa al’ummar musulmai su ɗau maganarsa cikin waɗannan mutum biyun ?