Labaran Duniya

Atiku Bai Yi Allah Wadai Da Kisan Da Aka Yi Wa Wadda Ta Yi Batanci Ga Annabi SAW Ba

SANARWA TA MUSAMMAN: Atiku Bai Yi Allah Wadai Da Kisan Da Aka Yi Wa Wadda Ta Yi Batanci Ga Annabi SAW Ba

Alhaji Atiku Abubakar ya kori mai kula da shafukan sada zumuntar sa biyo bayan wani rubutu da ya yi ba tare da izinin sa ba, ba kuma tare da izinin ofishin dake kula da watsa labaran sa ba.

Kamar yadda aka sani, Alhaji Atiku Abubakar ya rubuta a shafinsa na Instagram, Twitter da Facebook cewa duk wani rubutu da ba a ga A.A a karshen sa ba, to ba daga gurinsa ya fito ba. Daga gurin ma’aikatan sa ne, masu kula da kafofin sadarwa.

A karshe Alhaji Atiku Abubakar yana bada hakuri akan wannan rubutun da ma’aikacin sa ya yi.

Daga Muhammad Sunusi Hassan (Abban Hajia)
Director Media, ASO.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button