Labaran Kannywood

Video Abubuwa 3 Da Za A Rika Tunawa Da Daraktan ‘Izzar So’ Nura Mustapha Waye

Assalamualaikum warahamatullahi wabarkatuhu barkan a kowane lokaci a tashar Mai albarka ta hausablogng

Yadda a yau muka zo muku da wani sabon rahoto akan wasu abubuwan da baza, a  taba mantawa dasu ba a rayuwar nura mustapha waye

Ya dade a masana’antar shirya fina-fanai ta KANNYWOOD:

Izzar So ba shine fin na farko ba na Marigayi Nura Mustapha ba. Marigayin ya dade da shiga masana’antar ta Kannywood tun shekarar 2001. Ya  kuma yi fina-finai da dama.

Lakabin WAYE a sunansa

Ana yi wa marigayin lakabi da WAYE ne saboda da shi ne fim dinsa farko, wanda a bisa al’adar ‘yan masana’antar ana yi wa mutum lakabi da wani fim da ya fara yi, ko kuma ya yi suna a cikinsa.

Ilimin addini da kuma mu’amalla ta gari

Marigayi Nura makarancin Al kura’ni ne da kuma littafina yabo na manzon Allah (SAW) Dala’ilu khairat.

A cewar Balarabe Tela, “ko a ranar da zai rasu sai da ya yi karatunsa na Qur’ani da Dala’ilu kamar yadda ya saba a kullum.

“Sakamakon ilimin addini da ya taso da shi Hakan kuma ya tasirantu matuka a fim dinsa na Izzar So.”

Balarabe ya kuma ce, marigayin ya na da mu’amala mai kyau da jama’a, ba wai a Kannywood ba, hatta a unguwarsu ta Goron Dutse mutane sun ji rasuwarsa sosai soboda kyakyakyawar mu’amallarsa.

Muna matukar godiya da bibiyar mu a kowane lokaci a tashar Mai albarka ta hausablogng

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button