Wannan Itace sana’ar Jaruman kannywood kafin Daukaka Tazo musu

Wannan Itace sana’ar Jaruman kannywood kafin Daukaka Tazo musu
Allah mai iko kowa da akwai inda Allah ya tsaga masa inda zaici abinci dayawa jaruman kannywood ba sana’ar film suka fara ba sai daga baya suka shigo sana’ar kuma ta karɓe su
Kamar yadda muka sani yawancin jarumai maza a kannywood yan boko ne sai da suka gama karatun boko da suka ga babu ci abokon sai suka shigo harkar wasan kwaikwayo
Wasu kuma sana’ar kasuwanci suke wasu kuma sana’ar hannun kowa dai da akwai sana’ar daya fara kafin wasan kwaikwayo sannan ta karɓe su har sukayi arziki da ita
An bayyana Mawaki hamisu breaker Wanda yayi sana’ar ɗinkin kafin waka sai kuma mawaki ado gwanja wanda yayi sana’ar saida shayi kafin waka sai jaruma Maryam Yahaya data siyar da waina kafin ta fara Film
Suna da yawa wayan duk dai sunyi sana’o’i da dama kafin harkar film Wanda daga bisani kuma suka zama hanshakan masu kudi acikin masana’antar kannywood