Labaran Kannywood

Yan kannuwood da yan Daudu ma suke zabar shugaba Balle malami , Sheikh Idris yayi raga raga

Yan kannuwood da yan Daudu ma suke zabar shugaba Balle malami , Sheikh Idris yayi raga raga

Wani babban malami daga jihar Kaduna yayi raga raga da Mutanen da suke zargin malami akan siyasa cewa suna zuwa suna karbo kudi domin suyi zabe kuma su saka mutanen domin zabar ra’ayin su

Read Also

Sai dai malamin ya dauki zafi acikin karatun nasa wanda ake ganin kamar ya fadawa yan kannywood magana da kuma yan daudu wanda abin yakawo masa cece kuce da zage zage daga bangarori biyun

Malamin yace ya kamata mutane su bar malamai su hutu komai sai kaji an ce malami sai kace shi kadai ne zai iya fadar gaskiya bayan kowa yana da kunne yana da bakin dazai iya yiwa gwabnayi korafi amma mutane sunyi shiru sai malamai suke jira wai dole sune zasu fadawa gwabnati gaskiya

Inda yace indai zabe ne babu abinda zai hana malamai yin rijistar zabe balle yin zaɓe domin sunema suka chanchanci suyi zabe ba wani yayinda yace yan kannywood ma da yan daudu sukayi zabe balle malami

Wannan maganar ce kuma take ciwa yan kannywood tuwo a kwarya inda sukace lallai malamin nan ya raina musu hankali sukenan basu da daraja a duniya dahar zaiyi irin wannan misalin akansu?

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button