Labaran Kannywood

Tofa ! Tsakanin presdo da Lukman waye zai kai sumayya kasar wajen domin ayi mata aiki

Tofa ! Tsakanin presdo da Lukman waye zai kai sumayya kasar wajen domin ayi mata aiki

 

Read Also

Wannan shirin a kullum kara rikita mutane akeyi daga a nuna wannan shine babban masoyin sumayya sai kuma daga baya a nuna ai wannan yafi kowa muhimmanci akan ta masu kallo dai suna biye da wannan shirin zasuga har inda za’a kaishi domin kawo karshen komai acikinsa

Tun lokacin da sumayya ta samu matsala a fuskarta shikke duka wa’yannan masoyan nata biyu suka rikice domin ganin kowa daga cikin su shine yayi wannan gwanintar ta daukar dawainiyar maganinta sai dai kuma kowa daga cikin su yanada karfi ma’ana yana da kudi babu wanda zaka iya nunawa kace shine yafi kudi acikin susu biyun

Yanzu sumayya tana bukatar kulawa daga garesu duka su biyun amma kuma yanzu ba lokacin taladdima bane lokacine wanda zasu dubi halin da take ciki domin kawo mata dauki cikin gaggawa

Tundai da sumayya ta samu wannan larurar ake yar rige rige tsakanin presdo da Lukman wajen ganin sun nuna mata soyayya ta hakika a cikin wannan halin da take ciki domin anan ne zata fahimci waye masoyi ta na gaskiya a tsakaninsu

Presdo yana amfani da karfin kudi da kuma karfin jiki wajen ganin ya kawo duk wata kulawa ga sumayya inda shi kuma Lukman yake amfani da fahimta da basira wajen shima ya nuna abinda presdo yake kokarin yi

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button