Kunji abinda jaruma Rahama sadau tace akan kasancewarta gwarzuwar jarumar kannywood

Kunji abinda jaruma Rahama sadau tace akan kasancewarta gwarzuwar jarumar kannywood
Tun sanda aka bayyana cewa jaruma Rahama sadau itace jaruma wacce tafi kowacce jaruma kwazo da kokari acikin masana’antar kannywood shikkenan wannan jarumar darajar ta ta kara sama akan sauran jarumai wanda kuma daman ta bayyana tun abaya cewa bawai kokari da kwazo ta bane ya janyo mata kawai dai Allah ne ya kadda kuma dole ta gode masa
Sannan ta fadi yadda zasuyi iya bakin kokarinsu wajen ganin sun kara daga darajar wasan Hausa Domin shine yayi musu rana dan haka bazasu taba mantawa da wannan harkar ba koda kuwa me suka zama a wannan diniyar
Sannan jarumar tayi kira ga yan uwanta sauran jarumai akan su kara dagewa wajen ganin suka sun kai wannan matakin da takai wanda tace dole sai anyi aiki tukuru sannan Allah yake bayar da nasara
A yadda jaruma rahama sadau tayi magana duk yadda kakai ga bakasonta dole ta birgeka saboda tayi bayani cikin nutsuwa da kuma hankali shi yasa ma a yanzu ake ganin ta gama da sauran jarumai wajen iya mu’amala da gogewa a harkar Film