Innanillahi wa’inna i’laihir raji’un Allah yayiwa fitaccen jarumin kannywood rasuwa wanda ake kira da Awarwasa

Innanillahi wa’inna i’laihir raji’un Allah yayiwa fitaccen jarumin kannywood rasuwa wanda ake kira da Awarwasa
Allah yajikansa da rahama yasa aljanna ce makomarsa wannan jarumin a yanzu a cikin jarumai shima yana daga cikin wanda tauraruwarsu take matukar haskawa saboda irin gudummawar da suke bayarwa a irin role din da suke fitowa harya fara zama wani shima a kannywood sai gashi lokaci yazo Allah ya dauke abinsa
Wannan abin yanzu yasa duka yan kannywood jikinsu ya fara sanyi saboda irin dauki daidai da mutuwa ta fara yi musu sati Daya kenan da rasuwar kamal Aboki saiga shima wannan Allah yayi masa rasuwa
Jarumi acikin shiri mai nisan zango wanda yana daga cikin jigon wannan shirin irin yadda mutane suke jin dadin kallonsa a wannan shiri saboda irin aikin da yake wajen tura sako inda ya kamata
Dole aji tsoron Allah saboda babu wanda yasan ranar dazai mutu Allah yasa idan tamu tazo mu cika da imani an bayyana a safiyar yau za’ayo jana’izar wannan jarumin a garin jos