Jaruma Jamila nagudu da danta Mus’ab a kasa mai Tsarki abin ya birge masoyanta

Jaruma Jamila nagudu da danta Mus’ab a kasa mai Tsarki abin ya birge masoyanta
Jarumar ta dauki lokaci mai tarin yawa a masana’antar kannywood tana aikin Film dan haka wasu daga cikin jaruman kannywood suke girmamata domin ta fisu girma da kuma gogewa a wannan fagen
Abinda zai baku mamaki kuma har yanzu shine yadda jarumar take wasu abubuwan kamar wata karamar yarinya wanda hakan ya nuna cewa har yanzu dai tanaji da samartaka dan haka zata iya duk wani abu da kananan jarumai sukeyi
Sai dai bayyanar wannan hoton na jarumar da danta yasa wasu suke mata kallon tsohu wanda a yanzu duk wani abu da zatayi bazata kayatar da mutane ba domin yanzu akan iya kintatan shekarunta
Acikin video tana tare da dan da kuma mahaifiyarta wanda ta dauki nauyin biya musu domin ziyartar dakin Allah da kuma ibada Allah yasaka mata da alkhairi
Babu shakka duk mai kyautatawa iyaye bazai tabeta ba wannan shine sirrin da yasa wannan jarumar ta dauki lokaci mai tsayi tana jan zarenta acikin kannywood