Yadda mutuwar jarumi Awarwasa ta girgiza jaruman kannywood

Yadda mutuwar jarumi Awarwasa ta girgiza jaruman kannywood
Innanillahi wa’inna i’laihir raji’un babu shakka jaruman kannywood suna cikin tashin hankali saboda mutuwar wannan jarumin wanda tasa duk jikinsu yayi sanyi saboda kowa yasan cewa mutuwa ba wasa ba dan haka muka kawo muku yadda wasu daga cikin jarumai suke fada
A zahirin gaskiya babu wani jarumi wanda ya nuna tashin hankalinsa kamar jarumin na cikin shirin Aduniya wanda kusan shine jarumin daya fara nuna Awarwasa acikin finafinan sa har yakai yanzu duniya ta Sansa wato tijjani Asasu
Jarumai da dama san samu zuwa wannan wajen na rasu wanda wasu suka dinga kuka saboda yadda mutuwa take musu dauki dai dai
Babban abinda ya kamata suyi masa shine addu’a saboda mutuwa an riga anyi kuma bazai taba dawowaba dan haka muke addu’ar Allah yajikansa da rahama yasa aljanna ce makomarsa Ameen